Friday 23 January 2026 - 01:32
Duk Wani Hari ga Jagoran Juyin Juya Hali Hukuncin Kisa Ne / Ban San Abin da Yasa Mutane Na Musamman Da Suka Yi Shiru Me Suke Tunani ba?

Hauza/ Mai girma Ayatullah Nuri Hamadani ya fayyace cewa: "Ya kamata shugaban kasar Amurka ya sani cewa duk wanda ke son kai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci hari hukuncin kisa ne a kansa. Mun riga mun bayyana dalilan shari'a akan hakan. Muna daukar goyon bayan jagora a matsayin wani wajibi na addini.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Nuri Hamadani a wata ganawa da ya yi da limaman lardin Tehran ya yi la'akari da cewa ayyukan malamai yana da matukar muhimmanci da tasiri inda ya bayyana cewa: "Muna cikin wani zamani na musamman kuma a yau makiya suna yin amfani da yanar gizo wajen dukkanin hare-haren da suke kai wa malamai, don haka ya kamata su ma malamai su kasance a fagen. A yau aikin Limamai ba kawai saka abaya da jan Sallah ba ne amma ba ruwansu da halin da jama’a suke ciki, bai kamata malamai su bar dandalin ba."

Mai girma, da yake yin kakkausar suka ga shirun da manyan mutane na musamman suka yi wajen tayar da zaune tsaye ko kuma lattin daukar matsaya, ya ce: "Ban san me 'yan uwa ke tunani ba? Shin suna ganin idan aka ruguza Jamhuriyyar Musulunci makiya za su bar sauran wani abu daga Allah, Kur'ani da Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su)? Duk mun ga abin da suka yi wa mutane da masallatai da wuraren ibada a lokacin fitinar da ta faru a baya-bayan nan. Yadda suka kona Alkur'ani."

Ya ci gaba da cewa: "Shin da gaske ne duk wadannan abubuwan saboda matsalar tattalin arziki ne? Babu shakka, mutane suna cikin mawuyacin hali na rayuwa, amma masu aikata laifukan da suka kashe mutane tare da kona komai ba daga cikin mutane suke ba."

Wannan babban marja'i ya kara da cewa: "Shugaban kasar Amurka a hukumance yana goya wa masu tada tarzoma baya tare da yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci barazana. Tabbas bai cancanci amsa ba, amma ya kamata ya sani cewa Ayatullah Khamenei a matsayinsa na masanin fikihu kuma jagoran al'umma duk wanda yake son kai masa hari to hukuncin kisa ne a kan sa. Ba mu dauki goyon bayan jagora a matsayin wani lamari na siyasa ba kawai, sai dai wajibin addini ne."

Ayatullah Nuri Hamadani ya ci gaba da cewa: "Idan na ga wasu sun yi shiru a cikin fitina ko yin sharhi a makare suna jiran su ga yadda zata kaya, sai na yi mamaki, musamman a lokacin da gaskiya da karya suke a bayyane."

Wannan marja'i ya fayyace cewa: "Ba mu da tantama akwai bukatar a samu hadin kai a kasar, kuma kada a samu sabani, amma wannan ba dalili ba ne da zai sa wasu su yi duk abin da suka ga dama, kowa ya yi shiru, ko kuma hukumar da ke sa ido ta kasa sanya ido a ce muna son a samu hadin kai."

A karshe Ayatullah Nuri Hamadani ya jaddada cewa: "Hadin kai yana nufin taimakawa wajen magance matsalolin mutane. Jagoran juyin juya hali ya ce, "ya kamata jami'ai su rubanya aikinsu" wato su kara himma wajen gudanar da ayyukansu, wato bangaren shari'a a fannin shari'a, majalisar da ke sa ido da kuma bangaren zartarwa wajen warware matsalolin jama'a ba dare da rana."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha